1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shin dakarun SADC za su samu galaba kan 'yan tawayen M23?

Martina Schwikowski AMA/SB
May 14, 2024

Rundunar hadin gwiwa ta kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kudancin Afirka na aiki tukuri dan wanzar da zaman lafiya da murkushe 'yan tawayen M23 a yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/4fq1v
Rundunar hadin gwiwa ta kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kudancin Afirka
Rundunar hadin gwiwa ta kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kudancin AfirkaHoto: AUBIN MUKONI/AFP

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na buga kirji da kawancen sojan kungiyar hadaka ta SADC don magance tashe-tashen hankulan da suka yi kamari a yankin gabashin kasar. Kungiyar 'yan tawayen M23 ta fara fara kaddamar hare-harenta ne a zangon farko na shekarar 2022 da ta gabata kan dakarun sojan Kwango a sansanin da suka ja daga kusa da iyakokin Ruwanda da Yuganda, lamarin da ya haifar da dumbin 'yan gudun hijira.

Karin Bayani: Kwango: M23 ta karbe iko da mahakar ma'adinai ta Rubaya

Rundunar hadin gwiwa ta kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kudancin Afirka
Rundunar hadin gwiwa ta kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kudancin AfirkaHoto: ALFREDO ZUNIGA/AFP

Sai dai masu sharhi na ganin da kamar wuya sojojin hada kan SADC su iya murkushe 'yan tawayen M23 kamar yadda kasar Kwangon ke ta fafutika, ganin irin yadda suka kasa yin wani abin azo a gani a yankuna da dama na kasashen Kudancin Afirka, kana batun kudaden tafiyar da ayyukan dakarun ma na daga ciki in ji Stephanie Wolters, mai bincike a babbar cibiyar da ke sa ido kan harkokin waje ta kasar Afirka ta Kudu. Sannan Stephanie Wolters ta bayar da karin misali ga irin matsalolin da rundunar ta fuskanta a kasar Mozambik, wace aka girke tun shekarar 2021 da zummar tallafa wa dakarun kasar yakar 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi a yakin Cabo Delgado na Mozambik. Sai dai shekaru bayan kafa ta, rundunar na fuskantar tarnaki a yankin bisa rashin isassun kudi na gudanarwa.

Gabashin Kwango mai fama da rikici
Gabashin Kwango mai fama da rikiciHoto: Moses Sawasawa/AP Photo/picture alliance

Akwai dai yuwuwar yaki ya barke a tsakanin kasashen da Rwanda idan har runndunar SADE ta kasance a Kwango duba da yadda kasar Amurka da tarayyar Afirka suka zargi Ruwanda da hannu kai tsaye wajen tallafa wa dakarun 'yan tawayen M23. Masu sharhi dai na hasashen akwai yiwuwar samun kudaden tallafion da za a dauki nauyin rundunar tsaron ta kasashen SADC a kasar daga bangarorin kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya. Yanzu haka dai yakin da ake gwabzawa tsakanin gwamnatin Kwango da dakarun 'yan tawayen M23, ya haddasa miliyoyin 'yan gudun hijira da kuma kisan dubban fararen hula.